1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin IS na kai hare-hare a Turkiyya

Ahmed SalisuFebruary 19, 2015

Rahotanni daga Turkiyya na cewa akwai yiwuwar 'yan kungiyar nan ta IS su aiwatar da hare-hare a birnin Istambul da na Ankata da ke kasar Turkiyya.

Symbolbild Islamischer Staat
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kafafen watsa labaran Turkiyya din sun rawaito hukumar leken asirin kasar na cewar dubban 'yan IS din na kokarin shiga kasar ta kudanci domin kame wasu yankuna da nufin maida su karkashin ikonsu da ma aiwatar da hare-hare.

Baya ga wannan, kafofin watsa labaran sun kuma ce akwai yiwuwar 'yan kungiyar ta IS din su danna cikin kasashe irinsu Bulgariya da makamantansu don kaddamar da hare-hare a wasu kasashen dake cikin kungiyar tarayyar Turai.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kawacen da sojin Amirka ke jagoranta ke cigaba da kai hare-hare kan mayakan IS din da nufin karya kashin bayansu.