1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shirin Jamus na mayar da bakin haure na samun karbuwa

Suleiman Babayo MAB
February 2, 2026

Shirin Mayar da bakin haure kasashensu bisa radin kai na Jamus na kara samun karbuwa inda bakin haure ke komawa gida.

Bakin haure da 'yan gudun hijira a Jamus
Bakin haure da 'yan gudun hijira a JamusHoto: Johannes Simon/Getty Images


Ana kara samun bakin haure da suka amince da shirin komawa gida domin radin kansu daga kasar Jamus inda a shekara ta 2024 aka samu fiye da 10,300 na mutanen da suka yi amfanin da wannan damar karkashin shirin gwamnati.

Tasirin shirin

Bakin haure da 'yan gudun hijira a JamusHoto: Gero Breloer/AP Photo/picture alliance

Sannan a shekarar da ta gabata ta 2025 alkaluman wadanda suka koma kasashensu domin radin kansu daga Jamus sun haura 16,500, kamar yadda ofishin kula da 'yan gudun hijira na kasar ya tabbatar.

Babban abin da ya taimaka wajen mayar da 'yan gudun hijira da bakin haure zuwa gida shi ne kawo karshen yakin da ke faruwa a Siriya. Ministan kula da harkokin cikin gida na Jamus Alexander Dobrindt ya ce shirin gwamnatin na mayar da bakin haure kasashensu yana kara samun karbuwa da kuma tasiri.