Isra'ila: Dage kafa gwamnatin hadaka
June 4, 2021Haka kwatsam ne dai kakakin majalisar ta Isra'ila ta Knesset, Yariv Levin na jam'iyar Likud ta Benjamin Netanjahu ya sanar da cewa, sai wani lokaci da ba a fayyace ba a makon da ke tafe, majalisar za ta yi zaman kada kuri'ar amince wa ko akasin haka da sabuwar gwamnatin ta 'yan adawa da akewa take da Hukumar Sauyi. Wanna dai ya sanya 'yan adawa na ganin matakin a matsayin wani yunkuri na bai wa Netanyahu damar wargaza kawance.
Karin Bayani: Masar za ta shiga tsaknin Isra'ila da Falasdinu
Dama dai tuni Netanyahu ya gayyaci taron gaggawa na kusoshin jam'iyyarsa ta Likud, domin tattauna abin da ya kira kokarin hana jefa Isra'ila cikin ramin halaka: "Abu guda nake sake nanatawa shi ne, abun takaici ne ace masu akidar kare Isra'ila daga barazanar ciki da waje, za su hada kawance da masu sassaucin ra'ayin da ba abun da ya dame su bayan hawa kan kujerar mulki. Idan mu kai haka, mun tafka kuskuren da tsawon tarihi ba za a manta da aikata wannan aikin ta'asar ba."
A cewar Gabi Ashkenazi na jam'iyyar Yamina daya daga cikin jam'iyu takwas da ke cikin kawancen sabuwar hukumar da Naftali Bennett zai jagoranta da walakin wai goro a miya, kan irin jan kafar da majalisar ke yi wajen amince wa da hukumar. Tuni dai sabon shugaban gwamnatin da ke jiran amincewar majalisa, Bennett ya bayyana yadda majalisar ministocinsa za ta kasance. A karon farko ya ce zai cika wa gamayyar jam'iyyun Larabawa alkawarinsu na ba su gurbun kujerar minista guda. Idan har hakan ta tabbata, zai kasance karo na farko a tarihin Isra'ila da aka nada Balarabe minista sakamakon kawancen jam'iyyu.
Karin Bayani: An rusa majalisar dokokin Isra'ila
A hannu guda kuma, gamayyar jam'iyyun Larabawan da suka shiga wannan kawance karkashin jagorancin Abbas Mansur na kare kansu da shiga cikin wannan kawancen kan cewa, sun yi hakan ne domin kyautata rayuwar Larabawan Isra'ila, yadda sabuwar gwamnatin ta yi musu alkawarin ware musu makudan kudi domin raya kauyukansu. Wadannan dalilan dai, sun sanya jami'yyun Larabawa masu akidar gurguzu na cewa alkawarin muzuru ne.