1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Shirin kafa gwamnatin hadaka tsakanin jam'iyyun Pakistan

Zainab Mohammed Abubakar
February 12, 2024

Zaben da aka yi a Pakistan a makon jiya ya bar baya da kura kasancewar babu wata jam’iyya da ta samu isassun kujeru a majalisar domin kafa gwamnati ita kadai.

Hoto: PPI/Zuma/picture alliance

Ana ci gaba da shawarwarin kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyar tsohon Firaminista Nawaz Sharif mai kujeru 75 da kuma jam'iyyar Bilawal Bhutto Zardari mai kujeru 54 da kuma wasu kananan jam'iyyu.

'Yan takara masu zaman kansu da ke samun goyon bayan tsohon Firaminista Imran Khan da ke daure a gidan yari, sun sami mafi yawan kujeru 93 kuma suna fafatawa don kafa gwamnati.

An yi takarar kujeru 264 daga cikin jimillar kujeru 336 na majalisar. Akwai kuma wasu kujeru 70 da aka kebe.