1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karin harajin kayayyaki da kashi 7.5

Uwais Abubakar Idris RGB
November 22, 2019

Yunkurin karin kudin haraji kan kayayyaki da gwamnatin Najeriya ta yi shelara yi, ya janyo cece-kuce da koke daga akasarin talakawan kasar da ke cewa za su fada cikin kuncin rayuwa muddun aka aiwatar da shirin.

Nigeria Abuja -  Muhammadu Buhari nach Rückkehr aus England
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency Handout

A Najeriya  amincewar da majalisar dattawan kasar ta yi kan karin harajin kayayyaki daga kashi 5 zuwa kasha 7.5 ya sanya maida murtani daga ‘yan Najeriya da  duba tasirin da wannan zai a fanin ci gtaban kasar da kuma halin rayuwa da alumma ke ciki. Shugaban majalisar dattawan kasar ne ya jagoranci sauran ‘yan majalisar, inda suka amince da dokar karin harajin kayayyaki a kasar. Lamarin da ke nufin, daga watan Janairun badi, harajin kayayyakin na VAT zai karu da kashi 2.5 zuwa kashi 7.5 a kasar.

Kungiyar Kwadagon kasar ta ce akwai lauje cikin nadi a shirin yin karin harajinHoto: dapd

Wannan mataki ya kawo karshen jan ido da masu adawa da karin ke yi a kasar bisa fargabar, zai iya haifara da hauhawan kayayyaki.
To sai dai a bangaren masu goyon bayan matakin a majalisar, suna nuna cewa abin da fa gwamnatin ke shirin yi shi ne kara haraji a kan kayayyaki na kawa ba wai alummar Najeriyar ne abin zai shafa ba, matakin da mafi yawan ‘yayan jam'iyyar adawa ta PDP a majlisar suka ki amincewa.
Tuni  Kungiyar Kwadago ta ULC ta bayyana rashin amincewarta da wannan kari bisa cewa tana tababa a kan dalilin yin karin. Najeriyar dai na daya daga cikin kasashen da ke karbar harajin kayayyakli mafi kankanta, amma kwararru na bayyana cewa, kwatanta kasar da wasu kasashe ba adalci bane, domin kamata ya yi a duba karfin tattalin arziki ga al'ummar kasar.