1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shin kasashen AES za su fice daga kotun ICC?

Salissou Boukari SB
September 17, 2025

A Jamhuriyar Nijar, kasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar sun nuna shirinsu na shirin ficewa daga kotun kasa da kasa ta ICC. Labarin ya bayyana ne yayin wani zaman taro da ministocin shari'a na kasashen uku.

Mali Bamako 2025 | Tutocin kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da ke kungiyar AES
Tutocin kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da ke kungiyar AESHoto: Makan Fofana/DW

A Jamhuriyar Nijar, kasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar sun nuna shirinsu na shirin ficewa daga kotun kasa da kasa ta ICC. Labarin ya bayyana ne yayin wani zaman taro da ministocin shari'a na kasashen uku da ke cikin kawancen kasashen yankin Sahel na (AES) suka gudanar a birnin Yamai, wanda suke fatan maye gurbinta da wata kotun da za ta hukunta masu manyan laifuka ta Sahel.

Lokacin taron

Mutum mutumin shugabannin kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso da ke kungiyar AESHoto: Makan Fofana/DW

A yayin zaman taron nasu na birnin Yamai, ministocin shari'a na kasashen na uku na AES, sun dukufa wajen sa ido kan aiwatar da shawarwarin da aka bayar a taron birnin Bamako da ya gudana a watan mayu da ya gabata. Ciki har da batun sake nazarin hadin gwiwa na shari'a a game da masu manyan laifuffuka na kasa da kasa tsakanin kasashen na ESA da sauran kasashen duniya, ko tsakanin hukumomin shari'a, ko ma kungiyoyi na kasa da kasa.

Kuma ganin cewa taro na Bamako ya tanadi kafa kotun da za ta hukunta masu manyan laifuka ta yankin Sahel ta AES ana ganin ita ce za ta maye gurbin kungiyar ta kasa da kasa ta ICC idan suka fice daga cikinta, koma da yake acewar Elfred Emanuel, masanin dokokin kasa da kasa idan ma kasashen na AES na da wannan aniya dokokin da suka kafa kotun ICC sun bada izinin fita ga wanda yake bukata:

Dalilin batun

Alamar kungiyar AES da ta kunshi kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina FasoHoto: GOUSNO/AFP via Getty Images

Duk da cewa batun ficewar kasashen Afrika daga wannan kotu batu ne da ya dade ana yin shi, amma kuma wasu na ganin cewa kasancewar kotun na sanya shugabanni da dama ko wasu masu karfi cizawa da busawa yayin gudanar da mulkinsu, inda a wasu kasashen wasu magabatan ke karyawa inda babu gaba musamman kan masu adawa.

Ga kungiyar nan ta G25 Nijar ta masu adawa da juyin mulkin da ya wakana a Jamhuriyar Nijar, ta bakin mai magana da yayun kungiyar Tahirou Garka, na ganin ita dai shari'a komai dadewa tana iya kama mai laifi a duk inda ya shiga.

ICC da Afirka

Ficewar Nijar daga rundunar tsaron MNJTF

03:40

This browser does not support the video element.

Sai dai ganin yadda daman kotun ta ICC da ke hukunta masu manyan laifuka, ta dade tana shan suka daga manyan 'yan fafutika masu kishin Afirka da ke ganin kotun a matsayin kotun da aka yi don gurfanar da 'yan Afirka. Daukan wannan mataki daga kasashen AES na yankin Sahel bai zama wani abin mamaki ba a cewar Dokta Atto Namaiwa, Malamin koyar da dokokin shari'a wanda ke ganin duk kotun da za a samar adalcinta ne zai sa a samu yarda da ita.

Taron ministocin kasashen uku ya kuma duba batutuwan da suka shafi karfafa haɗin gwiwar shari'a, da kuma tsaro a gidan yari ta hanyar yin nazari da rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyoyin da suka shafi taimakon juna na shari'a a cikin batutuwan da suka shafi laifuka, da kuma batun mika mutanen da aka yanke wa hukunci.