EU da Chaina na shirin kulla yarjejeniya
June 22, 2020Tun bayan sabanin da aka samu a tsakanin Kungiyar tarayyar Turai da Chaina bayan bullar annobar Coronavirus, a wannan Litinin bangarorin biyu sun amince su gudanar da wani taro don dinke barakar, ganawar da za a yi ta kafar bidiyo, za ta mayar da hankali kan yadda za su sabunta batun bunkasa dama kulla yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu.
A baya shirin ya fuskanci tsaiko bisa zargin Chainan da EU ta yi na sabawa dokokin kasa da kasa, kan matakinta a rikicin yankin Hong Kong da zarginta da yada labaran karya na cewa, gwamnatocin kasashen na EU sun gaza a yakar annobar Coronavirus, gwamnatin Beijing dai, ta musanta wadannan zarge-zargen.
Taron na yau, zai hada da Shugabar hukumar zartaswa ta EU Ursula von der Leyen da Shugaban majalisar Turan Charles Michel da kuma Shugaba Xi Jinping da Firaiminista Li Keqiang.