1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin musayar firsinoni tsakanin Isra'ila da Hamas

October 17, 2011

Isra'ila ta sanar da sunayen firsinonin Falisɗinu 447 a matsayin yanki na shirin musayar firsinoni tsakaninta da ƙungiyar Hamas

Bafalisɗine ɗauke da tutocin da za a kawata gari da su kafin zuwan firsinoniHoto: dapd

Ƙasar Isra'ila ta fara shirya sakin firsinonin Falisɗinu da za ta yi musayarsu tare da ƙungiyar Hamas. Sama da firsinonin Falisɗinu ɗari huɗu aka kwasa zuwa wani sansani da ke yankin hamadar Negev inda za a yi musayarsu a gobe Talata da sojan Isra'ila, Gilad Shalit wanda aka kame shekaru biyar da suka gabata. Firsinonin Falisɗinu sama da dubu guda ne dai Isra'ila za ta sake su cikin watanni biyu masu zuwa. A ranar Lahadi, 16.10.2011 sai da Isra'ilar ta sanar da sunayen Falisɗinawa 447 da da za ta sakesu. Ɗaruruwan Falisɗinawa ne dai Isra'ila ke tsare da su bisa laifin kai munanan hare hare akanta. To sai dai al'umar Isra'ila na bayyana matuƙar damuwarsu game da wannan yarjejrniya da suke kallo a matsayin abin da zai kawo cikas ga aikin tsaro.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi