Shirin nukiliyar Iran bai yi nisa kamar yadda ake fargaba ba
December 4, 2007Wani nazari da hukumomin leƙen asirin Amirka suka yi ya gano cewa fargabar da ake yi cewar Iran na kera makaman nukiliya a ɓoye, ba ta kai yadda ake zato ba. Wani rahoto da hukumomin leƙen asirin 16 suka bayar ya yi nuni da cewa tun a ƙarshen shekara ta 2003 Iran ta katse shirye shiryen ta na nukiliya kuma ba ta fafaɗo da shi ba har zuwa tsakiyar wannan shekara. Hukumomin suka ce dalilin dakatar da shirye shiryen shi ne matsin lamba da kuma yawaita sa ido da ƙasashen duniya ke yiwa hukumomin birnin Teheran. Mai bawa shugaba Bush shawara akan harkokin tsaro Stephen Hadley ya ce gwamnatin Amirka na ganin rahoton a matsayin shaida ta manufofin ta dangane da ƙara matsawa Iran kaimi hade da bin hanyoyin diplomasiya da ƙasashen duniya ke yi don warware rikicin nukiliyar da ake yi da Iran.
“Rahoton wani labari ne mai kyau. A hannu ɗaya ya ba mu gaskiya dangane da damuwar mu akan hankoron Iran na ƙera makaman nukiliya. Sannan a daya hannu ya nunar ad cewa muin samun ci-gaba a ƙoƙarin daƙile wannan shiri na Iran.”