Shirin Obama a kan Siriya na samun nasara
September 5, 2013Kwamitin harkokin wajen majalisar dattawan Amirka, ya kaɗa ƙuri'ar amincewa da shirin shugaba Obama na kaiwa ƙasar Siriya farmakin soji, inda aka zargi gwamnatin Siriya da yin amfani da makamai masu guba. Ƙudurin ya amince da yin amfani da soji domin kai farmaki na tsawon kwanaki 90, amma ya haramta tura sojojin Amirka a cikin ƙasar ta Siriya. Shugaba Obama a yanzu haka yana a ƙasashen Turai gabanin taron ƙungiyar ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya da aka sani da G20, inda zai gana da shugabannin ƙasashen China da Japan. Obama dai yana kan yin lallama ce ta samun goyon bayan ƙasashen duniya, bisa manufarsa ta kai farmaki a Siriya, abinda ƙasar Rasha ke matuƙar adawa da shi. Ƙasar China tace farmakin da soja daga ƙasashen waje a kan Siriya, zai yi matuƙar illa ga tattalin arzikin duniya baki ɗaya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamed Awal Balarabe