1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin rabon katocin zabe a Jamhuriyar Nijar

Mahaman KantaJanuary 21, 2016

Hukumar zaben Jamhuriyar Nijar CENI ta sanar da soma rabon katunan zabe daga ranar Alhamis 21 ga watan Janairu a kaf fadin kasar da ma kasashen waje.

Hoto: picture-alliance/dpa/Tife Owolabi

Tuni dai aka fara jigilan katoci a duk fadin kasar ta Nijar inda aka kafa kwamitin da ya hada jam'iyyun siyasa na ko wane bangare. Katocin dai ana rarrabasu ne a harabar gidanjan masu garuruwa, ko unguwanni, to sai dai tuni 'yan siyasar suka fara hannun ka mai sanda kan iri-irin matsaloli da ake fuskanta wajan raba katunan kamar yadda Moutala mahamoudou wani kusa a jam'iyyar MNSD Nasara ta adawa ya yi tsokaci:

"Irin matsalolin da ake fuskanta dai su ne wasu wuraran sai mutane su ki zuwa daukan katocinsu, wasu kuma ana samun masu boye takardu da gangan, amma kuma suna kiran 'yan siyasa da sauran wadanda wannan nauyi ya rataya a kansu da su yi taka tsan-tsan dan ganin duk wani mai kati ta shiga hannunsa domin idan babu katin zabe to babu zabe sannan matsala ta biyu ita ce sai mutane sun yi hattara domin akwai masu sayan katocin zabe kamar yadda aka gani ga wancan zabe da ya gabata."

Hoto: DW/M. Kanta

Sai dai a cewar Ali Ibou daya daga cikin membobin kawancan jam'iyyun da ke mulki na MNR nashi tsokaci ya yi kan wannan batu yana mai cewa:

" Shidai kwamitin da aka kafa ya kumshi dukannin bangarori na 'yan siyasa kuma a duk inda suka kai katuna za su kidaya ko katuna nawa suka baiwa mai gari ko mai unguwa da dai wadanda ke da nauyin karbar wadannan katoci domin rabonta. Idan kuma sun yi aiki yini guda sun tashi, kafin su bar wurin sai sun kidaya sun ga katoci nawa suka rage, kuma idan sun dawo da safe haka nan kafin su fara aiki rarrabawa, sai kuma sun kidaya sun gani ko katoci nawa ne don haka ni ban ga inda za a ce za a sayi kati domin mutunj idan ba katinsa ba ne to ba za a ba shi ba."

Hoto: DW

Bayan ma batun rabon kati wani abun da akasarin mutane ke nuna shakku a kanshi shi ne batun gyaran kuraran da aka gano a cikin kundin rajistan masu zabe wanda kwararru na kungiyar OIF ta kasashe masu amfani da harshen Faransanci suka gudanar kamar yadda Annobo Sumaila da ke bangaran jam'iyyun da ke tsakiya ya yi tsokaci

" To mu korafin da muke ba raba katunan ba, wasu na kokawa da cewa katocin ma da aka bugo babu sunayansu, kuma ko gyaran da aka ce an yi ba a saka sunayansu ba kenan akwai matsala, domin muddin mutun bai samu katinsa ba, to babu batun ya yi zabe, kuma mutane na tambayarmu batun gyaran da aka yi kuma muma mun yi tambaya amma ba'a bamu amsa ba. kenan bamu da tabbacin cewa an gyara wadannan kurakuran da OIF ta ce a gyara."

Wata ayar tambaya da jama'a ke yi ita ce ko hukumar zaben kasar ta Nijar ta yi amfani da shawarwarin da wakillan hukumar ta OIF ta bayar na cewa a wallafa jerin sunayan 'yan kasar da ke bisa kundin rajistan masu zabe a Internet ta yadda kowa zai iya dubawa, tare ma da tantance ko wace runfa zai yi zabe, da kuma batun ake wa da sakonni na SMS ga wadanda suka bayar da lambobinsu a lokacin rajistan masu zabe ta yadda za a sanar da su inda runfarsu na zabe suke.