1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Zelensky na shirin sake ganawa da Trump

December 27, 2025

Ganawar na zuwa a daidai lokacin da Rasha ke kara matsa kaimi wajen yin awon gaba da karin wasu yankunan Ukraine masu matukar mahimmanci.

USA New York 2025 | Treffen zwischen Donald Trump und Wolodymyr Selenskyj bei der UN-Generalversammlung
Hoto: POU/ROPI/picture alliance

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai gana a gobe Lahadi da takwaransa na Amurka Donald Trump a Florida.

Shugabannin biyu za su tattauna kan batu mai sarkakiya na sakar wa Rasha yankunan Ukraine da ta mamaye a kokarin kawo karshen yakin da har kawo wannan lokaci tattaunawar sulhu ta ci tura.

Karin bayani: Hanyar neman tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine

A cewar mista Zelensky, muhimman batutuwa da za su mayar da hankali a kai sun hada da mokomar yankin Donbas mai arzikin masana'antu da ma'adinai da Rasha ke ikirarin kwacewa da kuma tashar nukiliya ta Zaporizhzhia da ke hannun sojojin Moscow.

Gabannin wannan ganawa da Trump, shugaba Zelensky ya tattauna da shugabanni da dama ciki har da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da kuma sakataren kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW