1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sayar da kadarorin gwamnatin Najeriya na cikin rudani

September 27, 2016

A Najeriya kungiyar kwadagon kasar ta ce za ta yi fito na fito da gwamnati a kan shirin sayar da kadarorin gwamnatin kasar domin ceto tattalin arziki daga hali na koma baya.

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Yanayi na koma baya da ke fuskantar tattalin arzikin Najeriya ya sanya tado da batun sayar da kadarorin gwamnati domin samun kudadden gudanarwa musamman na aiwatar da kasafin kudin kasar abin da kungiyar kwadago ta ce ba ta hango mafita daga abin da ta kira rashin dabara. Comrade Nuhu Abbayo Toro jigo a kungiyar kwadago kana mataimaki na musamman ga shugaban kungiyar, wanda ba za su goyo bayan shirin gwamnatin ba.

Hoto: Reuters/A. Sotunde

Tuni dama wannan lamari na ci gaba da haifar da cece-kuce a kasar musamman ganin  kara shiga yanayi na halin wahalar tattalin arziki. Alhaji Shattima  Umar Abba Gana shi ne shugaban hukumar kula da tattara kudadden shiga da rarrabasu ta Najeriya ya ce a yi taka tsantsan.

To sai dai  a yayain da wasu masana tattalin arziki ke kashedi ga gwamnatin  da ta guji tunanen daukan wannan mataki, ga Mallam Abubakar Ali masani a kan tattalin arzikin Najeriya na mai bayyana cewa ba a nan ma matsalar take ba.

Hoto: Reuters

Tuni dai kwarrau a fanin tattalin arzikin irin su Farfaesa Charles Sulodo ke bayyana tunanen sayar da kadarorin gwamnatin a matsayin babban kuskure, har zuwa wannan lokacin shugaban Najeriya bai ce komai ba kan wannan batu.