Shirin sayer da abinci a farashi mai rahusa a Nijar
March 4, 2026
An yi bukin ne a karkashin jagorancin ministan kasuwanci da kamfanoni na kasa Abduolaye Saidu na tonne dubu 82 na abinci ne kamar shinkafa da masara da hatsi da sukari ne za a sayar da rahusa a fadin kasa.
Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kashe sojoji sa kai a Nijar
Game da tsarin sake gina kasa gwamnati a karkashin kampanin ta na ajiye abinci OPVN suka dauki alkawarin ajiye abinci mai yawa a kamfanin don 'yan kasa su samu wadataccen abinci kuma da rahussa musamman ma a watan nan na Ramadana. Wannan kuma abinci ne da kasa ta saya da kudinta.
Karin bayani: Zagayen mambonin majalisar mashawarta ta Jamhuriyar Nijar
Wannan bukin dai an yi shi ne a gaban shugabanin al'umma, wanda a cewar ajama'a abincin ya zo daidai lokacin da suke bukatarsa. Babban farin cikin al'uma game da sayer da abincin a farashi mai rahusa na da riba biyu, na farko a cewarsu su saya da arha kuma na biyu abinda suka noma ne da kansu inji Alkassoum Liman Ahar daya daga jagororin wakilan al'uma na gargajiya.
Karin bayani: Kuncin rayuwa na ma'aikatan gwamnati a Nijar
A karshe dai gwamnati a ta bakin ministan kasuwanci Abdoulaye Saidou cewa yayi sun dauki kwararan matakai na ganin abinci musamman ma a wanan wata na Ramadan ya wadata ga al'uma da ya kamata su anfana da wannan rahusa tare da yaki da yadda a ke kara ma masu karfi karfi da kuma yaki da karamcin abinci a kasa baki daya.