Shirin SPD na kalubalantar Merkel a 2013
September 29, 2012![Nordrhein-Westfalen/ Der designierte Spitzenkandidat der SPD fuer die Bundestagswahl 2013, Peer Steinbrueck, spricht am Samstag (29.09.12) in Muenster beim Parteitag der nordrhein-westfaelischen SPD. Auf der Tagesordnung des Parteitags steht unter anderem die Neuwahl des Landesvorstandes. (zu dapd-Text) Foto: Sascha Schuermann/dapd.](https://static.dw.com/image/16273354_800.webp)
Talla
Dan takarar da jamiyar adawa ta SPD ta tsayar a zaben gama gari da zai gudana a shekara mai zuwa a Jamus Peer Steinbrück ya ce jam'iyar ba zata yi kawance da ta CDU dake mulki ba in har ta sha kayi a zaben da zai gudana shekara mai zuwa. Steinbrück ya ce ba zai fuskanci taranaki wajen cimma manufofinsa a duk wata gwamnati da Angela Merkel zata jagoiranta.
Ya fadin haka ne a babban taron da jamiyarsa ta SPD ta gudanar a garin Münster dake nan jihar Nordrhein Westphalen. Steinbrück ya kuma jaddada cewa babu wata baraka da za a samun tsakanin shi da Sigmar Gabriel da Frank Walter Steinmeier dake jan ragamar jam'iyar.
Mawallafi: Halimatu Abbas
Edita: Mouhamadou Awal