1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin taron G20 ya kankama a Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe
July 6, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus za ta dauki bakuncin taron koli na kasashe 20 da suka fi karfin masana'antu a duniya a ranakun Jumma'a da Asabar a birnin Hamburg.

Deutschland - Die Hamburger Messe - Schauplatz des G20-Gipfel
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Heimken

Shugabar gwamnantin Jamus Angela Merkel ta daukin bakuncin taruka na koli iri daban-daban a cikin shekaru 12 da ta shafe a kan karagar mulki. Ita ce ta kasance mai masaukin baki a taron na kasashe takwas da suka fi karfin masana'antu a  2007, yayin da a shekara ta 2015 kuwa ta shirya taron kasashe bakwai da ke ji da kansu a fannin tattalin arziki a birnin Elmau. Sai dai taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da za ta dauki bakwanci da kuma zai gudana a birnin Hamburg zai ninka sauran tarurrukan a fannin yawan shugabanni. Sai dai baya ga adadin shugabannin, rashin samun daidaito tsakaninsu kan muhimman al'amura da ke ci wa duniya tuwo na zama wani kalubale ga Angela Merkel.

Angela Merkel da Moon Jae-in shugaban Koriya ta KuduHoto: Reuters/M. Tantussi

Taron G20 zai gudana a bana a wani yanayi na musamman. A kawai ayyukan ta'adanci, sauyin yanayi, nuna son kai a fannin cinikayya, kuma duk wadannan batutuwan na cikin ajandar taron. Duniya na cikin hargitsi saboda rarrabuwar kawuna da ake fuskanta.

Shugabanni uku da ake samun sabanin ra'ayi da su sun hada da na Amirka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, da kuma na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, kuma dukkaninsu za su halarci taron na G20 domin kare wasu muradunsu. Shugaba Erdogan ga misali zai yi amfani da taron Hamburg wajen yi wa Turkawa mazauna Jamus jawabi. Sai dai mahukunta sun haramta wannan gangami. Shi kuwa Trump na Amirka zai gana da Putin na Rasha a karon farko don tattauwa kan rikicin Ukraine da na Siriya.

Shugaba Trump da mai dakinsa Hoto: Reuters/A. Schmidt

A daya hannun kuma shugaban na Amirka zai jadadda matsayinsa na kare guraben aiki a kasarsa. Sai dai zai sake shan suka kan fitar da Amirka daga yarjejeniyar kare muhalli ta Paris da ake ta cece kuce a kanta. Ko da wani kwararren na kungiyar kare muhalli ta Green Peace Andree Boehling, sai da ya bukaci shugabar gwamnatin Jamus da ta kara azama wajen yaki da hayaki mai guba.

Taswirar Kasashen G20

Daya daga cikin abubuwan da Jamus ta sa gaba a taron G20 shi ne karfafa hulda da kasashen Afirka. hasali ma dai ta na son yin amfani da wani tsari da ta yi wa lakabi da "Compact with Afrika" wajen kwadaita wa masu hannu da shuni zuwa zuba jari a Afirka domin tattalin arzikinta ya bunkasa, maimakon dogaro da take yi kan taimakon raya kasa. 'Yan jarida dubu hudu da dari takwas da suka fito daga kasashen 65 na duniya ne za su bibiya taron kolin G20 a birnin na Hamburg.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani