1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tsagaita wuta ya ruguje a Sudan

May 11, 2012

Rashin shata kan iyakokin ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu ya sa yankin ya zama wani wuri da ba zai rabu da rikice rikice ba.

Image #: 17572235 Rebels from Sudan's Nuba Mountains pick through an exploded munitions truck of the Sudanese government after a battle in the town of Tess. Alan Boswell/MCT /LANDOV
Hoto: picture alliance/landov

"Bayan lokaci mai tsawo na zaman lafiya da juna, yanzu wani yaƙi ya ɓarke tsakanin ƙabilun yankin Nuba mai cike da tsaunuka na ƙasar Sudan. A cikin watan janerun shekarar 2002 a ƙasar Switzerland aka yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin na Nuba. Yarjejeniyar dai ta kasance zakaran gwajin dafi kuma abin misali ga wanzuwar zaman lafiya a ilahirin ƙasar Sudan, amma yau shekaru 10 bayan an koma fagen daga a yankin baki ɗaya."

Ita ma jaridar Neues Deutschland tsokaci ta yi game da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da take tangan-tangan, tana mai nuni da wani sabon yunƙurin Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da zaman lafiya a yankin kan iyakar Sudan da Sudan ta Kudu.

"Rashin shata kan iyakokin ƙasashen biyu ya sa yankin ya zama wani wuri da ba zai rabu da rikici ba. Duk da cewa kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira ga Sudan da Sudan ta Kudu da su janye dakarunsu daga yankin dake kewaye da Abyei mako guda bayan zartas da wani ƙuduri akan yankin, amma ana saka ayar tambaya game da girmama wannan wa'adi. Duk mda cewa Sudan ta Kudu ta nuna shirin komawa kan teburin sulhu, amma tana nuna shakku game da shawarwarin da tarayyar Afirka ta bayar na warware rikicin. Hatta a wannan makon ma an ba wa hamata iska a yankin, rikicin da ya fi shafar al'umar farar hula."

Buƙatar tattauna tsakanin marikitar Mali

Muna buƙatar tattaunawa da Abzinawa, inji jaridar Die Tageszeitung tana mai rawaito Francois Alfonsi wani wakilin ƙasar Faransa a majalisar dokokin Turai. Jaridar ta ce shi dai Alfonsi ɗan jam'iyar Corsa mai ƙawance da jam'iyar The Greens yana adawa da amfani da ƙarfin wajen warware rikicin Abzinawa a ƙasar Mali. Sai dai a cewar jaridar mahunkunta a birnin Bamako na ganin duk wata tattaunawa da 'yan awaren tambar amincewa da manufarsu ce ta yin fgito na fito, domin an sha tattaunawa da 'yan tawayen na Abzinawa, inda a shekarun 1992 da 2006 aka ƙulla yarjeniyoyin zaman lafiya amma ba a mutunta su ba. Sai dai yanzu da yake an shiga wani rikici, kamata yayi a nemo hanyoyin sulhu da za su samu karɓuwa daga sassan dake rikici da juna."

Hoto: AP

Ƙarafen tsaffin jiragen ruwa na barazana ga muhalli

Daga rikicin tawaye sai na muhalli. A rahoton da ta rubuta jaridar Die Welt ta mayar da hankali ne a halin da ake ciki a gaɓar tekun Legas dake tarayyar Najeriya, inda tarkacen wasu jiragen ruwa 77 ke janyo wani bala'i ga kewaye ɗan Adam da kuma tattalin arzikin jihar.

Hoto: picture-alliance/dpa

"Gwamnati na ƙoƙarin kawar da wannan shara ta ƙarafen jirgin ruwa sai dai yankin na gaɓar tekun da ya zama wani jujin tsaffin jiragen ruwa yana gurɓata muhalli a ilahirin yankin baki ɗaya. Saboda haka ya zama wajibi a kawar da yawan dogon turanci dake kawo cikas ga shirin kwashe wannan shara."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe