Shirin tsuke bakin aljihu a Girka
August 22, 2012A cikin wata hirar da jaridar Bild da ake bugawa a Jamus ta yi tare da firay ministan Girka Antonis Samaras a wannan Larabar, ya buƙaci baiwa gwamnati sa ƙarin lokaci domin rage kuɗaɗen da take kashewa da kuma samar da sauye-sauyen da suka shafi tattalin arzikin ta. Samaras dai ya ce yana buƙatar samun damar gamsar da jami'an tarayyar Turai domin samun ƙarin kuɗaɗen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar sa daya faɗa cikin mawuyacin hali.
Furucin nasa ya zo ne kwanaki biyu kachal gabannin wani muhimmin taron da zai gudana a Jamus game da batun rikicin kuɗin.
Samarars dai zai fara yunƙurin neman ƙarin lokacin ne a wannan Larabar, tare da ganawa da shugaban ƙungiyar ministocin kula da harkokin kuɗi na gamayyar ƙasashen Turai da ke yin amfani da takardar kuɗin Euro Jean-Claude Junker, inda zai nuna masa cewar Girka na da kyakkyawan ƙudirin samar da sauye-sauyen da ake buƙata, waɗanda kuma 'yan ƙasar ke nuna adawa da su, amma kuma ta cancanci samun ƙarin lokaci.
Sai dai kuma ana sa ran Junker, wanda ke zama mafi ƙarfin faɗa-a ji a gamayyar ƙasashen, zai shaidawa Samaras cewar tilas ne Girka ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun ta kuma tana da taƙaitaccen lokaci ne na yin hakan.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala