Shirin tsuke bakin aljihun Girka
May 27, 2011Shugabanin siyasar Girka sun gaza cimma matsaya dangane da ƙarin matakan tsuƙe bakin aljihun da ya kamata su ɗauka domin kauce wa sake tsunduma cikin matsalolin bashi. Wannan dai na zaman wani ƙafar ungulu ga fatan da ƙasar ke da shi na samun kaso na biyar na euro milliyan dubu ɗari da goma da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Asusun ba da lamuni na duniya suka ƙudiri niyyar bai wa ƙasar a matsayin rance. Ita dai Girka na buƙatar kason euro milliyan dubu 12 a gaggauce a cikin watan Yuni mai zuwa, domin ta iya ta tayar da komaɗar tattalin arziƙinta.
Daga farko dai shugaban ƙasar Girkar ya gayyaci Frime Minista George Papandreou da shugabanin huɗu daga cikin jam'iyyun adawar ƙasar, a wani mataki na samun haɗin kan jam'iyyun s don ganin an gudanar da sauye-sauyen da suka dace, domin rage basussukan da ake bin ƙasar.
Mawallafiya: Pianado Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas