Shirin wanzar da zaman lafiya a Yankin Gabas Ta Tsakiya
December 22, 2007Talla
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɓukaci ƙasashen da su ka yi alƙawarin tallafawa yankin Falasɗinawa da su yi ƙoƙarin cika alƙawari. Yin hakan a cewar Jami´i mai kula da harkokin siyasa, Mr Lynn Pascoe, abune da zai taimakawa yankin daidaita sahu, a fannoni na siyasa da tattalin arziƙi. Ƙasashen dai sunyi alƙawarin tallafawa yankin na Falasɗinawa ne da Dolar Amirka sama da biliyan 7, a wani taron gidauniya da aka gudanar a makon daya gabata a birnin Faris na ƙasar Faransa. Tallafin a cewar rahotanni na daga cikin ƙoƙarin da ake ne na samun wanzuwar zaman lafiya a Yankin na Gabas ta tsakiya, musanmamma a tsakanin Israela da Falasɗinawa.