Shirin yiwa tsarin kiwon lafiyar Amirka garambawul
March 21, 2010Majalisar wakilan Amirka na shirin kaɗa ƙuri´a akan shirin shugaba Barak Obama na yiwa tsarin kiwon lafiyar ƙasar kwaskwarima, shirin da ake taƙaddama kansa. Bayan ya shafe sama da shekara guda yana ƙoƙarin shawo kan ´yan jam´iyar adawa ta Republicans, shugaba Obama na fatan samun ƙuri´u 216 da yake buƙata don zartas da wannan mataki da ake kace-nace kansa. Ko da yake ana sa rai ƙuri´ar za ta yi ƙarfi, amma an jiyo Obama na mai kyautata fatan cewa sabon tsarin zai samu amincewar ´yan majalisar. A lokacin da yake jawabi ga ´yan majalisar Obama cewa yayi.
"Ba ni za ku yiwa ba. Ba jam´iyar democrats za ku yiwa ba. A´a ku yiwa al´umar Amirka domin su ne ke son ganin an ɗauki wannan gagarumin matakin."
To sai dai a lokaci ɗaya shugaban ya amsa cewar gyarar fuskar da za a yi wa tsarin kiwon lafiya ba zai iya magance dukkan matsalolin da ke a ƙasa ba.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala