1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Rikicin Siyasa gabanin zabe

Salissou Boukari LMJ
September 8, 2020

A Jamhuriyar Nijar yayin da sannu a hankali a ke kusantar zabukan kasar, takaddama iri-iri na ci gaba da kunno kai ta rashin yarda tsakanin 'yan adawa da masu mulki.

Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar NijarHoto: AFP/I Sanogo

'Yan adawar dai sun sanar da matakinsu na kauracewa zaman tantance jerin sunayen masu zaben, inda aka gayyato kwararru na kungiyar OIF ta kasashe masu magana da harshen Faransanci. 'Yan adawar dai sun ce an hana kwararrunsu sanin abin da na'urar computer da za a yi amfani da ita ta kunsa.

Karin Bayani: Nijar: Zaben kananan hukumomi a Disamba

Za dai a iya cewa har yanzu tsugune ba ta kare ba a fagen rikicin siyasar na Jamhuriyar Nijar, ganin cewa har yanzu babu wata cikakkiyar fahimtar juna tsakanin 'yan adawar da masu mulki wajen shirye-shiryen zabukan kasar. 'Yan magana dai na cewa riga kafi yafi magani, domin kuwa tun yanzu ne ya kamata a zauna cikin daraja juna domin tsayar da cikakkar al'kilbla ta zuwa zabe ba tare da muguwar aniya daga kowane bangare ba.

Karin Bayani: Nijar: Cece-kuce kan zabe

Batun tantance sahihancin jerin sunayan masu zabe na zamani da ake kira girgam, shi ne ya baro baya da kura, inda 'yan adawa suka ce sam basu ga haske cikin lamarin ba.

Jagoran adawa Hama Amadou na cikin gamayyar kungiyar adawar Nijar Cap 2020-2021Hoto: picture-alliance/dpa/K. Gabbert

A cewar gamayyar 'yan adawar na Nijar na Cap 2020-2021, kauracewar da suka yi suna da cikakar hujja, inda suka bayar da musalin cewa a wata kasa ta ECOWAS a shekara ta 2019 duk da cewa kasar ba ta yi fadin kasar Nijar ba, kuma ba ta da yawan al'ummar Nijar, kungiyar OIF din ta shafe tsawon wata guda kafin ta kammala binciken tantance sahihancin jerin sunayan masu zaben. A cewarsu ta yaya cikin kwanaki biyar wannan kungiya za ta yi wannan aiki a Nijar, idan har ana son aiki mai inganci? 

Sai dai duk kokarin samun bangaran hukumar zabe mai zaman kanta ta CENI wadda ta sanar da ranakun zaben a Nijar da wakilin DW ya yi, ya ci tura, inda aka bayyana masa cewa ba za su yi magana ba muddin dai ba wannan bincike aka kammala ba. Haka zalika ya nemi jin ta bakin jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, amma suka suma ba za su ce komai kan wannan batu ba. Sai dai komi take ciki, lamarin na bukatar dubawa, domin ko taron kungiyar ECOWAS da kan shi ya yi jan hankali kan muhimmancin shirya zabe na gaskiya domin kaucewa rikici irin wanda ya faru a Mali bayan zabe.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani