1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen bikin 'yancin kan kudancin Sudan

July 8, 2011

Ko da yake yankin kudancin Sudan zai samun 'yancin kansa amma fa har yau tsugune ba ta ƙare ba dangane da rikicin yankin, musamman ma tsakanin ƙabilun da ya ƙunsa

Bikin samun 'yancin kan kudancin SudanHoto: picture alliance/dpa

A wannan makon dai babban abin da ya fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus shi ne shirye-shiryen da ake yi na gabatar da shagulgulan 'yancin kan kudancin Sudan, inda jaridar Die Zeit take cewar:

"Ko da yake kudancin Sudan ta zama ƙasa mai cikakken ikon cin gashin kanta, amma fa a haƙiƙa a yanzu take dangane da gwagwarmayar mallakar filaye tsakanin ƙabilun yankin da suka haɗa da Dinka da Shilluk da kuma Nuer. Tun da ake ma dai ba a taɓa samun cikakken haɗin kai tsakanin ƙabilun yankin ba inda a cikin shekaru 1990 aka sha fama da zub da jini tsakanin ƙungiyar SPLA dake da rinjayen 'yan ƙabilar Dinka a hannu guda da kuma Shilluk da Nuer a ɗaya hannun. Saɓani tsakanin waɗannan ƙabilun ya fi tsamari akan taƙaddama tsakanin arewaci da kudancin Sudan, inda alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna asarar rayukan mutane sama da 1500 sakamakon wannan saɓani tun abin da ya kama daga farkon wannan shekarar."

Matsaloli a gabacin Afirka na tsawwala matsalar guje-gujen hijiraHoto: AP

Kimanin 'yan gudun hijira metan ne daga ƙasar Sudan suka halaka lokacin da kwale-kwalensu ya kama wuta akan hanyarsu ta zuwa Saudi-Arabiya a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda ta ƙara da yin nuni da cewar ana daɗa samun muhimman dalilan na gudun hijira a gabacin Afirka amma fa da wuya 'yan gudun hijirar ke samun mafita domin ɗarewa tudun na tsira. Kimanin 'yan gudun hijira dubu tara daga Somaliya da kuma wasu dubu ashirin da bakwai daga Habasha suka kama hanyarsu zuwa ƙasar Yemen ya zuwa ƙarshen watan mayun da ya gabata, alhali ita kanta ƙasar na fama da yamutsi.

A yayinda ƙasashen Jamus da Switzerland ke fafutukar rufe tashoshinsu na makamashin nukiliya, a nasu ɓangaren ƙasashen Afirka sai ƙoƙari suke na samar da waɗannan tashoshi don dogara akansu wajen samun makamashi a cewar jaridar Neues Deutschland. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

Ƙasashen Afirka na fafutukar dogara kan tashoshin makamashin nukiliyaHoto: S.Shahrigian

"Ƙasar Maroko na fatan fara aiwatar da makamashin nukiliya a shekara ta 2017 a yayinda Namibiya ta tsayar da shekara ta 2018 game da wannan manufa. Su kuma ƙasashen Najeriya da Masar suna fatan kammala gina tashoshin nukiliyar ne nan da shekara ta 2020. Kai hatta ƙasashe irinsu Burundi da Kap Verde dake fama da talauci da ma Kongo da ba ta da zaman lafiya sun shiga inuwar hukumar makamashin nukiliya ta ƙasa da ƙasa IAEO a taƙaice. Ƙasashen na fafutukar dogara kan makamashin nukiliyar ne ba tare da sun ba da la'akari da irin haɗarin dake tattare da wannan salo na samun makamashi ba."

A cikin wata sabuwa kuma a daidai lokacin da ake gudanar da gasar ƙwallon ƙafa ta mata don cin kofin duniya, an rasa makomar wasu mata 'yan wasan ƙwallon ƙafar su 14 daga ƙasashen Kamaru da Togo, waɗanda suka shigo Jamus don wasu wasannin dabam, kamar yadda jaridar Der Tagesspiegel ta rawaito. Ko da yake idan an cafke su, 'yan wasan na da ikon neman mafakar siyasa, amma bisa ga dukkan alamu za a komar da su gida ne a cewar jaridar.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal