An gawo karshen nuna gawar Fafaroma
April 25, 2025
Fiye da mutane dubu-150 suka wuce ta gaban akwatin gawar Marigayi Fafaroma Francis shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya, wanda ake shirye-shiryen binne shi gobe Asabar (26.04.2025). Shugabannin kasashen duniya suna ciki masu zuwa wannan jana'iza. Akwai dubban mutane masu zaman makoki da ke ci gaba da kai ziyara zuwa fadar Vatican domin girmama marigayin. Yanzu haka an kawo karshen ganin wannan gawar.
Karin Bayani: Gawar Fafaroma Francis ta isa cocin St Peter domin ban-kwana
Shugabannin kasashen duniya da suka hada da Doinald Trump na Amurka da Volodymyr Zelensky na Ukraine, da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, da Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado Olaf Scholz, da Shugaba Luiz Inácio Lula da Silvana Brazil gami da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, shi ma Shugaba Javier Milei na Ajentina mahaifan marigayi Fafaroma yana cikin shugabannin na duniya da yanzu haka jiragen saman da suke ciki suka nufi birnin Roma na kasar Italiya, domin zuwa wannan jana'iza.