1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen jana'izar Nelson Mandela

December 6, 2013

Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya bar duniya bayan da ya yi fama da cutar huhu. Ya shafe shekaru a gidan yari sakamakon yaki da wariyar launin fata da ya yi.

Trauer um Nelson Mandela
Hoto: Reuters

Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya rasu a gidansa da ke Johannesburg bayan doguwar jinya na cutar huhu. Tun cikin watan Juni tsohon Shugaba Afirka ta Kudu Mandela kuma gwarzon yaƙi da mulkin nuna wariyar launin fata ne rashin lafiyarsa ta ƙara tabarbarewa. A shekarar 1993 Nelson Mandela tare da tsohon Shugaba Frederik de Klerk suka samu lambar yabo ta Nobel.Mandela ya kwashe tsawon shekaru 27 a gidan fursuna saboda neman kwato wa sauran 'yan ƙasar Afirka ta Kudu 'yanci.Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da mika sakon ta'aziyar rasuwar tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela, wanda ya yi gwagwarmaya mulkin nuna wariyar launin fata. A cikin sakonsa Shugaban Amirka Barack Obama ya ce, Mandela ya kawo sauyi a Afirka ta Kudu wanda ya sauya duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce, Mandela jarumi ne wajen tabbatar da adalci. Sannan tsohon Shugaban Amirka Bill Clinton da kuma firaministan Birtaniya David Cameron suka danganta Nelson Mandela da gwarzon gwagwarmayar tabbatar da 'yanci.Shugabannin ƙasashen Afirka na cikin wadanda suka nuna bakin-ciki da alhini bisa rasuwar tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela.Yanzu haka a ƙasashe da yawa ciki har da Amirka an sassauto da tutoci ƙasa-ƙasa, domin girmama Marigayi Nelson Mandela.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita: Pinado Abdu Waba