1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen kafa sabuwar ƙasa a kudancin Sudan

July 1, 2011

A halin da ake ciki yanzu ana aiki gadan-gadan a shirye-shiryen tabbatar da 'yancin kan kudancin Sudan ranar tara ga wata

Dubban 'yan kudancin Sudan ke ɗoki da murnar kafa sabuwar ƙasarsuHoto: AP

A mako mai zuwa ne dai yankin kudancin Sudan, kamar yadda aka shirya, zai samu cikakken ikon cin gashin kansa, inda zai ɓalle daga arewacin ƙasar. Dangane da haka jaridu da dama na Jamus suka mayar da hankali kan halin da ake ciki a yankin da kuma irin jan aikin dake gaban shuagabannin da zasu ja akalar makomar kudancin Sudan, kamar dai jaridar Die Zeit wadda take cewar:

'Yan gudun hijira a kudancin SudanHoto: DW

"Tun daga ranar tara ga wannan wata ne dai yankin kudancin Sudan zai zama wata ƙasa mai cikakken ikon cin gashin kanta tare da fadar mulkinta a Juba da kuma mazauna miliyan shida. Sai dai kuma sabuwar ƙasar, wadda ita ce ta baya-bayan nan da za a kafa a doron ƙasa, daidai da sauran ƙasashen nahiyar Afirka, babu haɗin kai tsakanin ƙabilunta da suka haɗa da Dinka da Nuer da kuma Shilluk dake gwagwarmayar kama madafun iko da juna. Babban aikin dake gaban sabbin shuagabannin dai shi ne warkar da tabon yaƙin da yankin ke fama da shi da kuma ƙoƙarin ɗinke dukkan ɓarakar dake tsakanin kudanci da arewacin Sudan."

A can maƙobciyar ƙasa ta Kongo kuwa sai ƙara shiga hali na ƙaƙa-nika-yi mutane ke yi sakamakon matakai na cin zarafin mata da tsaffin sojojin Hutu ke yi da kuma gargaɗin da 'yan Tutsi ke yi na gabatar da yaƙi a gabashin Kongo a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓe a ƙasar a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda ta ƙara da cewar shi kansa rukunin sojan ƙasar ya fara wargajewa sakamakon rashin jituwa tsakanin dakarun sojan da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na ƙasar.

Mata masu zanga-zanga akan tsadar rayuwa a SenegalHoto: AP

A can ƙasar Senegal ta yammacin Afirka, kamar yadda mujallar Der Spiegel ta rawaito, shugaban ƙasa Abdoulaye Wade, ya janye daga yunƙurinsa na canza daftarin tsarin mulkin ƙasar domin samun kafar yin ta zarce sakamakon adawa mai tsanani da ya fuskanta daga al'umar ƙasar. Da dai so samu ne da Abdoulaye Wade zai ƙaunaci ganin ya kasance Nelson Mandela na biyu a nahiyar Afirka. Amma fa abin da ya banbanta su shi ne kasancewar shi Nelson Mandela yana da goyan bayan jama'a matuƙa da aniya, a yayinda shi kuma shugaban na Senegal ke fama da adawarsu. A makon da ya wuce ma dai sai da dubban-dubatar mutane suka shiga zanga-zanga domin adawa da matsalar tsadar rayuwa. Hakan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya Abdoulaye Wade mai shekaru 85 da haifuwa, ya dakatar da shawararsa ta canza daftarin tsarin mulkin ƙasar don neman yin ta zarce kan karagar mulki.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu