1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa a Masar

April 2, 2012

Hukumomin sojin Masar sun yi afuwa ga al-Shater domin share masa fagen yin takarar shugabancin ƙasar.

epa02614306 Egyptian senior member of the Muslim Brotherhood Khairat al-Shater (C) greets supporters as he joins tens of thousands of Egyptians gathered in Tahrir square, Cairo, Egypt, 04 March 2011. Protests continued in Cairo despite announcment by the Egyptian Armed Forces on 03 March appointing Sharaf to replace the controversial Ahmed Shafiq. Demonstrators are waiting for the rest of their demands to be met, including the release of all political prisoners and the lifting of the state of emergency. EPA/MOHAMED OMAR
Khairat al-Shater yana ɗaga hannu ga magoya bayan saHoto: picture-alliance/dpa

Majalisar mulkin sojin ƙasar Masar ta sanar da yin afuwa ga mutumin da ƙungiyar nan da aka fi sani da suna Muslim Brotherhood ta 'yan uwa Musulmi ta zaɓa domin ya yi mata takarar shugabancin ƙasar wato Khairat al-Shater daga wasu laifuka biyun da aka yanke masa hukunci akansu a can baya. Wannan dai na zaman sharar fage ne gare shi domin yin takara a zaɓen shugaban ƙasar da zai gudana cikin watanni shidda masu zuwa. A ranar Asabar da ta gabata ce dai ƙungiyar ta 'yan-uwa Musulmi ta kawo ƙarshen wata da watannin da aka yi ana cece-kuce game da ɗan takarar da za ta fitar.

Mai shekaru 61 a duniya, al-Shater, wani fitaccen ɗan kasuwa ne kana ɗaya daga cikin mataimaka ukku na shugaban jam'iyyar. A shekara ta 1995 ne wata kotun soji a Masar ta yi masa shari'a tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar akan laifin sake farfaɗo da ayyukan ƙungiyar ta 'yan-uwa Musulmi ko kuma Muslim Brotherhood - a turance. An kuma sake yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a shekara ta 2007 bisa tuhumar da ta shafi samar da makamai da kuma bayar da horo ga wasu ɗaliban jami'a. An dai sallame shi daga gidan yari ne jim-kaɗan bayan da boren nuna adawa da gwamnati ya yi nasarar kifar da mulkin tsohon shugaban ƙasar ta Masar Hosni Mubarak a farko-farkon shekarar da ta gabata.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas