1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shirye-shiryen zaben 2023

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 16, 2023

A daidai lokacin da babban zabe ke kara karatowa a Tarayyar Najeriya, tashar DW na kawo muku rahotannin kan al'amuran da suka shafi rayuwar al'umma da ma fatan da al'ummar ke da shi a yayin da kuma bayan zaben.

Najeriya | Zabe | 2023
Dogayen layin ababen hawa, saboda karanci da tsadar man fetur a NajeriyaHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Kwan-gaba kwan-baya kan batun samar da wadatattun takardun Naira da aka sake fasalinsu da kuma daina karbar tsofaffin da aka sauya, na adaga cikin tarin matsalolin da masana ke cewa za su iya kawo nakasu ga babban zaben kasar da ke tafe. A karshen makon gobe ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki na kasar, sai dai baya ga matsalar karancin kudin akwai ma ta karancin man fetur.

Tuni dai al'ummar kasar da dama suka shiga halin tasku na rashin kudi da ya haifar da rashin abinci, wanda hakan ake ganin yana iya hana mutane da dama fita rumfunan zabe. Sai dai kuma a wani jawabi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar, ya nunar da cewa za a ci gaba da amfani da Naira 200 da ke zaman guda daga cikin tkardun kudin da aka sauya fasalinsu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna