Shirye-shiryen zaben shugaban kasa a Senegal
January 24, 2012Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade ya bayyana aniyarsa na tsayawa takara a zaben kasar wanda za'a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa, domin neman wa'adinsa na uku. Wannan mataki dai na tattare sarkakiya sakamakon wata kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar bayan da shugaban ya hau kujerar mulki a karon farko a shekarar 2000, inda tanadin ya kayyade wa'adin kowane shugaban kasa zuwa biyu kacal. To sai dai shugaban gangamin yakin neman zaben na Wade ya ce ya bada gaskiya cewa kotun tsarin mulkin kasar zata amince da hujjar da suka bayar, wacce ke cewa, ba za'a saka wa'adin mulkinsa na farko a cikin lissafi ba. Tuni dai masu adawa da kungiyoyin farar hula suka yi watsi da wannan hujja suka bukaci da a kiyaye tanadin kundin tsarin mulki. Manyan 'yan takarar da ke neman kujerar shugabancin kasar sun hada da tsoffin shugabani irinsu Moustapha Niasse, Idrissa Seck Macky Sall da mawakin nan mai suna Youssou Ndour da kuma dan adawan nan na Socialisrt Ousmane Tanor Dieng
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Usman Shehu Usman