1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shisha na barna a tsakanin matasa a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar GAT
March 20, 2018

Shigowar tabar zamani ta Shisha a Afirka, ya sanya karuwar yawan samari da ‘yan mata mashayan wannan taba, wannan kuwa duk da gargadin da hukumar lafiya ta yi kan yadda take yin illa ga lafiya.

Iran Wochengalerie KW 34
Hoto: Irna

Shigowar tukunyar tabar zamani ta Shisha, ya sanya karuwar yawan samari da ‘yan mata mashaya tabar dama sigarin latroni da aka fi sani da suna E-Sigrat. Kasar Ghana na daga cikin kasashen nahiyar Afirka da ake fuskantar yaduwar wannan taba ta Shisha wannan kuwa duk da gargadin da hukumar lafiya ta yi kan yadda take yin illa ga lafiyar matasa.

 

Amfani da tukunyar tabar zamani ta Shisha, abu ne da ya zama kamar yayi musamman tsakanin matasa maza da mata a kasashen Afirka da dama a shekarun baya bayan nan. Shishar dai daga asali ana sha ne don nishadi, wanda ya samo asali daga yankunan Larabawa da Asiya. Sai dai yanzu lamarin daban yake. Malam Lawal Madoro shi ne shugaban wata cibiyar kulawa da tarbiyar matasa mai suna Nigas Rehabilitation center a Kaduna:

" Ita Shisha a wajen masu amfani da ita wani abin sha ne mai sa rayuwa ta yi dadi, ga kamshi da ke bin jikinka har a cikin zufarka. Wani kuma idan ya sha ta za ya ji shi tamkar ya tafi duniyar sama yana ta yawace-yawace a cikin filawowi da dai sauran abubuwa na rayuwa mai kyau. Wani kuma idan ya sha ta ya kwanta bisa gado, sai ya ji kamar ana tilla shi sama ana cabe shi. Wannan ne ke birge shi. Wasu kuma kan murza tabar Wiwi a cikin shishar hayakin ya tashi su yi ta zukar shi"


To shin me ya sa ake shan wannan hayaki na tukunya. Farhana Yahya matashiyace da ke ta'ammali da Shisha:

Hoto: DW/L. Tarek

" Wasunmu sha'awa ce ke sa mu sha. Wasu na shiga shan ta dan gasar wani aboki da ya saye tashi. Akwai wadanda ke iya share maka awa 24 a saman Shisha, ko ni ina yin haka wani lokacin. Idan na sha ta kan bani caji, kana jin abu sama-sama. Kana sai ka ji ba ka so a dame ka"


Kamar yadda wadannan matasa suka bayyana, ana amfani da tukunyar ta Shisha ce wajen shan wasu sinadrai masu hatsari ga rayuwa kamar kwaya da hodar iblis. Ko mene ne illar hakan? Dr Saidu Zakariya likita ne a tarayyar Najeriya, kasar da ke zama daya daga cikin inda shan Shishar ta zama tamkar abun alfahari:

" Ita kwakwalwa tana amfani da abin da jini ya kai mata, kuma jinin da ya shiga cikin huhu , jini ne da ke da daraja sosai, domin a nan ne jinin ke dibar iska wanda jiki ke amfani da shi. To yayin da mutun ya shaki turirin Shisha ya shiga cikin huhu, akwai kananan hanyoyin iska a cikin huhun inda ake samun jini yana fitar abin da ba ya da kyau a cikin shi kuma yana dibar mai kyau kamar Oxygene. To in akwai shi a cikin wannan sinadarin, zai debe shi kai tsaye ya hada shi da abin da ke cikin jinin. To tun a nan za a iya samun wani canji ya gudana sabili da kemikal ne. To daga nan jinin ke zuwa zuciya wacce ita kuma ke harba shi ko'ina a cikin jiki. Wannan sidarin idan ya shiga zuciya ba mamaki ya fara yin banna a cikin zuciyar"


Yawancin matasa da ke amfani da Shishan kan fake da samun nishadi don kauce wata matsala, Dr Saidu wace irin shawara zaka baiwa irin wadannan matasa?