Nijar: Ziyarar Shugaba Bazoum a Berlin
July 8, 2021Tuni dai al'ummar Jamhuriyar ta Nijar suka fara bayyana mabambantan ra'ayoyi kan wannan ziyara ta Shugaba Bazoum Mohamed tare da yadda suke fatan hulda tsakanin Jamus da Nijar ta kasance a gaba. Jamus dai tun asali tana da kima mai yawa a idanun al'ummar Nijar, sakamakon manyan tsare-tsare da Jamus ta samar a Nijar ta hanyar hukumomin raya kasashe na Jamus din kamar GIZ ko KfW da makamantansu, domin taimaka wa wajen bunkasa yankunan karkara a fannoni na samar da ruwa da ilimi da sadarwa da kuma gudanar da mulki na gari.
Karin Bayani: Rashin tsaro da rayuwar yara a Sahel
Sai dai Bana Ibrahim wani dan kasar ta Nijar mai fafutuka a shafinsa na internet, ya nunar da cewa duk da a ra'ayinsa zai so Nijar ta yi kokarin dogaro da kanta ta hanyar arzikin da Allah ya hore mata, amma hulda tsakanin kasarsa da Jamus abun yabawa ne, domin babu cuta ba cutarwa.
A fannin bunkasa harkokin noma kuwa akwai maganar takin zamani, wanda a cewar Mamane Nouri shugaban kungiyar farar hulla da ke kare hakkin masu saye dan amfaninsu ta ADDC Wadata, Jamus na daga cikin kasashen da suka rattaba hannu kan wani tsarin da Nijar ta yi dangane da batun takin zamani. Ya ce ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu dangane da wannan tsari ba, ya kyautu Shugaba Bazoum ya sake nazarin wannan batu.
Karin Bayani: Kafa rundunar sintiri ta Turai a Sahel
Al'ummar Nijar da dama ne dai ke zaune yanzu haka a kasar Jamus, suna ayyukansu cikin kwanciyar hankali da bin dokokin kasa. Sai dai kuma wasu da dama sun bukaci dawowa gida domin bude masana'antar da za ta ba su damar zama cikin kasarsu. A halin yanzu dai kallo ya koma ga yadda huldar kasar ta Nijar da Jamus za ta kasance a nan gaba, ganin yadda shugaban na Nijar Bazoum Mohamed ke son kawo sauye-sauye masu tarin yawa ta yadda 'yan kasa za su rinka gani a kasa a duk wata hulda da zai yi tsakanin kasa da kasa musamman Jamus da ke a matsayin mafi karfin tattalin arziki a Tarayyar Turai.