1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Biden na ziyara a Kyiv

February 20, 2023

Shugaba Joe Biden na Amirka na ziyarar bazata a Ukraine a wani mataki na nuna goyon baya ga kasar yayin da take dab da cika shekara guda da fara yaki.

Shugaban kasar Amirka Joe Biden tare da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky
Hoto: Ukrainian Presidential Press Service/via REUTERS

A lokacin da yake ganawa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, shugaba Biden ya tuna irin fargabar da ake da ita a shekarar da ta gabata, na yiwuwar Rasha ta karbe ikon babban birnin Ukraine, sai dai a cewarsa har yanzu Kyiv na tsaye da kafafunta. Shugaba Biden ya kuma kara jadadda irin goyon bayan da Amirka ke bai wa Ukraine ya na mai cewa, Amirkawa na tare da su kana duniya ta na tare da su.

Shugaba Biden ya kuma sanar da karin tallafin dala miliyan 500 ga Ukraine baya ga wanda Amirka ta sanar da bayarwa a baya, wadanda suka hada da manyan tankokin yaki da kuma makaman kare kai daga hare-hare. Ziyarar ta shugaban Amirka, ta na zuwa ne yayin da shugaba Zelensky ke matsa lamba ga kawayensa kan gaggauta tura masa karin tallafin makamai da ma jiragen sama na yaki.