1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaba Biden zai gana da Donald Trump a fadar White House

Binta Aliyu Zurmi
November 10, 2024

Shugaba Joe Biden na Amurka zai gana da zababben shugaban kasar Donald Trump a ranar Laraba, bayan alkawarin mika mulki cikin tsanaki jim kadan bayan nasarar ta dan jamiyyar Republicans a zaben da ya gabata.

Joe Biden vs Donald Trump
Hoto: imago images

Fadar White House ta ce Shugaba Biden da Donald Trump za su gana ne da misalin karfe 11 na safe agogon Washington a Larabar, wanda ke daidai da karfe hudu na yammaci agogon GMT.

Donald Trump dai ya kafa tarihin sake samun nasara a zaben da aka yi a ranar Talatar da ta gabata, za kuma a rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairun badi a mtsayin shugaban Amurka na 47.

Shugaba Joe Biden dai ya janye daga takarar shugabancin kasar ne a cikin watan Yuli, saboda dalilai na shekaru kuma tuni ya taya Trump muranr lashe zaben.

Karin Bayani:Shugabannin duniya na taya Trump murnar lashe zabe