1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari ya nemi manoma su ciyar da kasa

May 25, 2020

A sakamakon yadda annobar Coronavirus ta lakume biliyoyin kudaden da kasar ke warewa domin sayo abinci daga waje, Shugaba Buhari ya kalubalanci manoman kasar kan noma abincin da zai wadatar da kasar a wannan karo.

Reisanbau in Nigeria
Hoto: DW/S. Duckstein

A sakamakon yadda annobar Coronavirus ta lakume biliyoyin kudaden da kasar ke warewa domin sayo abinci daga waje a kowace shekara domin cike gibin abinci da kasar ke bukata, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga manoman kasar da su tashi tsayin daka domin noma abincin da zai wadatar da al'ummar kasar. Kama daga madara ya zuwa nama da alkama da ma sauran bukatu na abinci dai, Tarrayar Najeriya kan kashe tsakanin Dalar Amirka miliyan dubu bakwai zuwa kusan 22 a shekara da zummar biyan bukatar ciyar da mutane miliyan kusan 200. To sai dai kuma annoba ta Corona da ta kai ga faduwar farashin man fetur dai, na neman jefa kasar cikin tsaka mai wuya ga bukatun na ciyar da kai mai tasiri ga 'yan kasar a halin yanzu.

Babu dai kudade na wajen da kasar ke fatan tana iya amfani da su wajen sayo kayan abincin da take bukata buka a fada ta shugaban kasar da ke aiken sako ga manoma na mikewa tsaye a kan hanyar sauyin tsari da nufin ceto daukacin al'ummar kasar.
Shugaban kasar dai ya ce ba zabi ga manoman face mikewa a tsaye da nufin kaiwa ga samar da abincin cikin gida maimakon dogaro da kasuwanni na waje da a baya suke taka rawa wajen ciyar da al'ummar Tarrayar Najeriyar da daman gaske.

Hoto: Getty Images/AFP/Y. Foly

Batun kaucewa yunwar dai na zaman daya a cikin hujjojin 'yan mulkin na yanke shawarar sake bude lamura, a daidai lokacin da annobar Covid-19 ke kara yaduwa tsakanin al'umma ta kasar. To sai dai har ya zuwa yanzu kuma a fadar Mohammed Magaji Gombe da ke zaman kakakin kungiyar manoma ta kasar, da akwai sauran aiki a tsakanin burin na ciyar da kan da ke zaman sabon kwazo a kasar da matakan 'yan mulki a sassa dabam-dabam na Tarrayar Najeriya da ke fakewa a cikin Covid-19 da nufin yi wa noman illa.

Da kyar da gumin goshi ne dai Abujar ta yi nasarar shawo kai na 'yan kasar wajen komawa noman shinkafa baya, abun kuma da ake ta'allakawa da rage radadin a zauna a gidan sakamakon annobar Covid-19. To sai dai kuma komai hobbasa ta manoman, batun rashin tsaron da ke tashi da lafawa a daukacin sassa na arewacin kasar da ma dagewa bisa tsohon tsarin noman na neman sake mai da hannun agogo a baya a tunanin Farfesa Ahmed Mohamed Bakori da ke zaman kwarrare a cikin harkar noman, musamman a arewacin kasar da ke zaman tungar noman Tarrayar Najeriyar.

Hoto: AP

Gwamnatin Najeriyar dai na cewa akwai shirin sabbin dabarun noman da ya kai kasar ga cin bashi na Dala miliyan sama da dubu daya a halin yanzu da nufin sayen motocin noma na zamani a lunguna da sakunan kasar da nufin habakar noman, amma a cikin tsarin da har yanzu ke zaman na takarda maimakon na zahirin da ke iya ceton al'ummar Najeriyar.