1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush na Amirka, ya tabbatad da cewa ƙungiyar leƙen asirin CIA na da sansanonin sirri, inda take tsare ’yan ta’adda.

September 7, 2006

Shugaban Amirka, George W. Bush, ya tabbatar a karo na farko cewa, ƙungiyar leƙen asirin ƙasarsa, wato CIA, ta daɗe tana tsare fursunonin da ake tuhumarsu da ta’addanci a sansanonin sirrinta. A cikin wani jawabinsa da aka buga a birnin Washington, shugaba Bush ya ce wasu mutane 14 da ake tuhumarsu da kasancewa ƙusoshin ƙungiyar al-Qaeda, waɗanda kuma ke tsare a waɗannan sansanonin, yanzu an mai da su sansanin Guantanamo Bay. Bush ya ƙara da cewa, tambayoyin da aka yi wa fursunonin sun hana aukuwar wasu sabbin hare-haren ƙunan baƙin wake. Kuma ba a gallaza musu ba a duk tsawon lokacin da ake bincikensu. A cikin fursunonin da aka mai da su sansanin Guantanamon dai har da Khalid Sheikh Mohammed, wanda ake zargi da shirya kai harin ƙunan bakin waken ran 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 a Amirkan.

Rahotannin da kafofin yaɗa labarai suka buga game da sansanonin sirrin na ƙungiyar CIA a wasu ƙasashen Turai dai, sun janyo hauhawar tsamari tsakanin Washington da ƙungiyar EU.