1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Bush ya isa kasar China a rangadin kasashen nahiyar Asiya

November 19, 2005

Shugaban Amirka GWB ya sauka a kasar China a mataki na 3 na rangadin da yake kaiwa kasashen nahiyar Asiya. A hukumance dai a gobe lahadi ne idan Allah Ya kaimu shugaban China Hu Jintao zai tarbi Bush din a wani faretin girmamawa na soji. Daga cikin batutuwan da shugabannin biyu zasu tattauna a kai har da huldar cinikaiya tsakanin China da Amirka da batun darajar takardun kudadensu sai yaki da annobar murar tsuntsaye da kuma shirin nukiliyar KTA da ake takaddama a kai. Ana sa ran cewa shugaba Bush zai tabo maganar kare hakin dan Adam a China.