1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHUGABA CHIRAC YA BUDE TARON KULLA HULDA DA AFIRKA A BIRNIN PARIS.

Yahaya Ahmed.November 11, 2003

Shugaba Jacques Chirac na Faransa, ya nanata kiransa ne ga gamayyar kasa da kasa da ta yi la'akari da cewar nahiyar Afirka fa tana muhimmanci kwarai a wannan sabon salo na hadayyar tattalin arzikin duniya. Nahiyar na bukatar matukar taimako don iya tsayawa da kafafunta a jerin sahun sauran kasashen baki daya. Muddin kuwa ba a bata wannan taimakon ba, to babu shakka, a wani lokaci nan gaba, wani mugun rikici zai iya barkewa wanda da wuya a iya shawo kansa.
Salon hadayyar tattalin arzikin duniya, ba zai ci nasara ba sai an taimaka wa Afirka ta farfado daga matsalolin da take huskanta, inji shugaba Chirac. Matasan nahiyar, su ne ma wadanda suka fi bukatar kulawa matuka. A dai yarje kan shirya wannan taron na kulla hulda da Afirka ne a lokacin taron kolin nan na kungiyar G 8, ta kasashe mafi arziki a duniya, da aka yi a cikin watan Yunin da ya gabata a garin Evian na kasar Faransa. kasashen kungiyar nan ta NEPAD wadanda suka hada da Aljeriya, da Masar, da Najeriya, da Senegal da Afirka ta Kudu ne suka wakilci nahiyar Afirka a taron.
Da yake amsa tambayoyin maneman labarai bayan jawabinsa, shugaban na Faransa, ya karfafa muhimmancin da akwai na kulawa da matasan nahiyar Afirka. Su dai wadannan matasan, inji shugaban, ba za su taba sa ido suna kallon yadda za a yi musu saniyar ware ba. Za su iya kasancewa wani mummunan bala'i ga duniya baki daya, idan aka yi watsi da maslaharsu, ko kuma idan aka ci zarafinsu. Sabili da haka ne yake ganin wajibi ne ga duk kasashe mawadata da su hada gwiwa, wajen inganta ci gaban da aka riga aka samu a nahiyar, musamman ma dai a huskar samad da zaman lafiya, a wasu wuraren yankunan. Babu shakka shugaban na matshiya ne da Jumhuriyar Dimukradiyya Ta Kwango, da Sudan, da Laberiya da kuma Angola.
A daya bangaren kuma, shugaba Chirac, ya yi kira ga kasashen nahiyar ta Afirka da su nuna dauriya wajen yakan cin hanci da rashawa da kuma tabbatad da hakkin dan adam. Ba za a iya samun ci gaba a duk wani matakin da za adauka ba, sai an sami yanayin da ya dace, inda za a sami haske a cikin duk huldodin da kasashe za su dinga yi da juna.
A taron kolin kasashen G 8 da aka yi a Evian dai, an karfafa cewa, za a dau matakan rage yawan talauci a duniya daga adadinsa na yanzu zuwa rabi kafin shekara ta 2015. A halin yanzu dai an kiyasci cewa, kusan mutane miliyan dubu da dari biyu ne ke rayuwa da kasa da dola daya a duniya, sa'annan, kusan miliyan dari 8 da 40 ne ke fama da yunwa. Yawan masu rashin ingantaccen ruwan sha a duniya kuwa ya kai miliyan dubu.
Bankin Duniya da Hukumar Lafiya ta duniya sun kiyasci cewa, za a bukaci karin kuddi na kimanin dola biliyan 50 a kowace shekara, idan ana son a cim ma wani sahihin sakamako a harkokin raya kasashe masu tasowa. Game da hakan kuwa, shhugaba Jacques Chirac ya dau alkawarin cewa, kasarsa za ta dau nauyin da ya rataya a wuyarta ta kuma aiwatad da matakan da suka dace don cim ma wannan manufar. Ya kuma bayyana cewa, kafin shekara ta 2012 Faransa ma za ta shiga rukunin kasashen nan da ke ba da kashi sifili da digo 7 na kudaden shigarsu a ko wace shekara, ga ayyukan raya kasa, a kasashe masu tasowa. A halin yanzu kuwa, wadannan kasashen sun hada ne da Dennmark, da Holland, da Norway, da Sweden da kuma Luxemburg.
Shugaba Chirac, ya kuma shawarci gamayyar kasa da kasa da su kirkiro wani haraji a kan duk wata ribar da za a samu a huldodin kasuwanci karkashin salon nan na globalisation. Kudaden shiga da za samu daga wannan harajin, za a yi amfani ne da su kacokan wajen ba da taimakon raya kasa ga kasashe masu tasowa. A matakin farko dai shugaban ya ba da sanarwar kafa wani kwamiti wanda zai yi nazarin aiwatad wannan shirin, wanda kuma zai mika masa rahotonsa a cikin watanni 6 masu zuwa.