1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Emmanuel Macron ya lashe zabe a Faransa

April 24, 2022

Alkaluman hasashen zabe a Faransa, sun nuna shugaba mai ci Emmanuel Macron ya doke abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen a zaben kasar da aka kammala.

Frankreich Präsidentschaftswahl | Jubel Macron-Anhänger
Hoto: LUDOVIC MARIN/AFP

Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa, ya lashe zaben kasar da aka kammala a yau Lahadi.  

Mr. Macron ya samu kashi 58.2% cikin dari ne cikin dari na kuri'un.

Abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen wadda ta amsa shan kaye, ta samu kashi 41.8% cikin dari.

'Yar takarar adawar, Marine Le Pen, ta lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya musamman ma wajen ganin ta taka rawa a zaben majalisar dokokin kasar da ke tafe.

Tuni ma shugabannin gwamnati da hukumomi da ma 'yan siyasar nahiyar Turai suka taya Shugaba Macron murnar sake lashe zaben na Faransa.