1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron zai tattauna batun Iran da shugabannin G7

Binta Aliyu Zurmi
March 11, 2026

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da shugabannin kasashen kungiyar G7 masu arzikin masana'antu a gaba a yau domin tattauna rikicin Iran da hauhawar farashin makamashi.

Kanada Kananaskis 2025 | G7 Gipfeltreffen - Treffen der EU Regierungchefs mit Mark Carney
Hoto: Simon Dawson/Avalon/IMAGO

Tattaunawar dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatocin kasashen G7 ke nazarin yadda za su mayar da martani kan hauhawar farashin man fetur sakamakon yakin da Amurka da Isra'ila suke yi da Iran. 

Ministocin makamashi na kasashen G7 sun yi jinkirin cimma matsaya kan manyan tsare-tsaren mai, a maimakon haka sun bukaci hukumar kula da makamashi ta duniya da ta tantance lamarin kafin daukar mataki. 

Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi da ba a ga irinsa ba a tsawon shekaru hudu, sai dai a ranar Talata farashin ya sauka da kusan kashi 11 cikin 100 bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi hasashen cewa yakin Gabas ta Tsakiya zai iya kawo karshe nan ba da jimawa ba

Faransa ce shugabar kungiyar G7 da ta hada da Amurka da Kanada da Japan da Italiya da Birtaniya da kuma Jamus.

 

Karin bayani: Farashin mai ya fadi