1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ziyarar shugaban Turkiyya a Jamus

November 17, 2023

Shugaba kasar Turkiyya na ziyara a Jamus. Ziyarar mai cike da sarkakiya na zuwa ne bayan kalamai da Erdogan ya yi a baya-bayan kan rikicin Isra'ila da Hamas a Gaza.

Erdogan na ziyara mai cike da cece-kuce a Jamus
Erdogan na ziyara mai cike da cece-kuce a JamusHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Kwanaki biyu gabanin fara ziyarar tasa da ke zama ta farko a Jamus a cikin shekaru uku, shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana Isra'ila a matsayin ''kasar 'yan ta'adda'' tare kuma da zargin Amurka da kawayenta na Yamma da daure wa Isra'ilar gindikan kisan kiyashin da ya ce tana yi wa al'ummar Falasdinu.

Karin bayani: Erdogan ya soki sabon rikicin Gabas ta Tsakiya

Wadannan kalamai sun haifar da tada jiyoyin wuya a Jamus inda kungiyoyi musamman ma na Yahudawa suka bukaci da a soke ziyarar, yayin da jam'iyyar adawa ta masu ra'ayin mazan jiya da kuma jam'iyyun kawancen gwamnati na FDP da Die Gren suka ce yanayin da ake ciki bai dace da ziyarar ba.

Karin bayani:  Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra'ila, tare da yanke duk wata hulda da Firminista Benjamin Netanyahu

Sai dai duk da wadannan kiraye-kiraye ba a soke ziyarar shugaban ba wanda zai samu tarbe daga shugaban gwamnati Olaf Scholz, kuma ana sa ran batun rikicin Gabas ta Tsakkiya da batun dakile kwararar bakin haure 'yan Siriya da kuma yakin Rasha da Ukraine za su mamaye tattaunar ta su.