1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSomaliya

Shugaba Erdogan ya soki lamirin hatta kasar Somaliland

Abdoulaye Mamane Amadou
December 30, 2025

Kwanaki bayan amincewa da yankin Somaliland a matsayin kasa da Isra'ila ta yi, kasar Turkiyya ta yi fatali da matakin tana mai bayyana shi a matsayin wanda bai dace ba.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHoto: Turkish Presidency/Murat Kula/Anadolu/picture alliance

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya bayyana cewa amincewar da Isra’ila ta yi wa yankin Somaliland a matsayin kasa mai cikakken 'yanci ko kadan bai dace da ka'ida ba, kana ya yi kira ga kasashen duniya da su yi watsi da shi da matakin.

Somaliya ta yi martani kan matsayar Isra'ila kan yankin Somaliland

Shugaban na Turkiyya ya bayyana hakane a yayin da yake karbar bakwancin takwaransa na kasar Somaliya wanda ke ziyarar aiki a birnin Istanbul.

Shugaba Erdogan ya ce, "Daukar matakin kare cikakken 'yancin Somaliya ta kowane hali na da matukar muhimmanci a gare mu. saboda haka, matakin da Isra’ila ta dauka na amincewa da Somaliland ba halattacce ba ne, kuma ba za a yarda da shi ba". a yayin da yake jawabi a gaban manema labarai.

Afirka ta soki na'am da Isra'ila ta yi da Somaliland

Yankin na Somaliland da ke fafutikar ballewa daga Somaliya, ya ayyana kansa a  matsayin kasa mai cin gashin kanta tun shekarar 1991 bayan barkewar wani wani mummunan rikici da ya kai ga darewar 'yan kasar gida biyu.