Shugaba Erdogan zai ziyarci Jamus
November 11, 2023
A yayin wannan ziyara da ke zama ta farko da Recep Tayyip Erdogan zai kawo Jamus cikin shekaru uku, shugaban zai gana da shugaban gwamnatin Olaf Scholz a ranar Juma'a mai zuwa kamar yadda kakakin gwamnatin ta Berlin ta tabbatar.
Karin bayani: Erdogan ya soki sabon rikicin Gabas ta Tsakiya
Wannan ziyara dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Turkiyya da membobin NATO a game da rikicin Isra'ila da Hamas wanda ya barke kwanaki 35 da suka gabata.
Tattaunawar shugabannin biyu za ta mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda kakakin gwamnatin Jamus ta shaida wa manema labarai.
Karin bayani: Turkiyya ta janye jakadanta daga Isra'ila, tare da yanke duk wata hulda da Firminista Benjamin Netanyahu
A baya dai mista Erdogan ya kakkausar suka ga Isra'ila tare da zarginta da aikata laifukan cin zarafin bil adama a zirin Gaza inda ya kirayi jakadan Turkiyya daga kasar don nuna bacin ransa.