1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Joe Biden ya janye daga takarar shugabancin kasa

Abdoulaye Mamane Amadou
July 21, 2024

Makwanni bayan cece-kuce da ban hakuri daga karshen shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa ya hakura ya janye daga takarar shugabancin kasar Amurka da zai kara da Donald Trump

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe BidenHoto: Susan Walsh/AP Photo/picture alliance

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa ya hakura, ya janye daga takarar zaben shugabancin kasa da za a yi a watan Nuwanban wannan shekara.

Mai shekaru 81 a duniya Joe Biden, ya bayyana cewa ya dauki matakin ne don kishin Amurka da kuma ci-gaban jam'iyyarsa ta Democrat, inda ya ce zai ci gaba da rike mukaminsa na shugaban Amurka har zuwa karshen wa'adin mulkinsa. Shafukan sada zumunta da dama ciki har da DW Hausa sun wallafa matakin shugaban da ya zo wa jama'a ba za ta.

Karin bayani : Donald Trump na kan hanyarsa ta zama shugaba

Ana dakon jawabin shugaban nan da wani lokaci don zayyana dalilansa na janyewa daga takara da za ta hada shi da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

An shafe makwanni ana ta kiraye-kirayen Shugaba Biden da ya janye daga takarar shugabancin kasar amma kuma ya yi mirsisin cewa ba zai janye ba, yana mai cewa shi kadai ke iya karawa da abokin hamayyarsa Donald Trump.

Karin bayani : Shugaban Amurka Joe Biden ya kamu da cutar Corona

Biden ya daga hannun mataimakiyarsa Kamala HarrisHoto: Tierney L. Cross/newscon/picture alliance

Shugaba Biden ya mika sunan mataimakiyarsa Kamala Harris matsayin wacce za ta gaje shi a takarar shugabancin kasar na watan Nuwamba.

Ana dakon mataki na gaba da jam'iyyar Democrat za ta dauka.