Shugaba Karzai ya tsallake rijiya da baya a wani harin ´yan Taliban
June 10, 2007Talla
Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya tsallake rijiya da baya a wani harin da ´yan Taliban suka kai da nufin halaka shi. Kakakin gwamnati a birnin Kabul ya ce ´yan tawayen Taliban sun harba rokoki akan wani taron jama´a a lardin Ghasni a lokacin da shugaba Karzai ke yiwa taron jawabi. To amma rokokin ba su fadi inda aka auna su ba kuma ba wanda ya ji rauni sakamakon harin. Wani kakakin kungiyar Taliban ya tabbatar da kai harin. A wani labarin kuma an kashe mayakan Taliban akalla 47 a wani kazamin fada da suka gwabza da ´yan sanda da sojojin Afghanistan da kuma dakarun dake karkashin jagorancin kungiyar tsaro ta NATO.