1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin gwamnoni a Sudan ta Kudu

Yusuf BalaDecember 30, 2015

Shugaba Kiir na Sudan ta Kudu ya ce dole ne sabbin gwamnonin su yi aiki da yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan adawa.

Südsudan Präsident Salva Kiir
Shugaba Salva KiiHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bukaci sabbin gwamnonin da aka nada a kasar su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi tsakanin gwamnatinsa da bangaren 'yan adawa a karshen watan Agusta.

Da yake jawabi a lokacin rantsar da sabbin gwamnonin a ranar Talata shugab Kiir ya bayyana cewa ba zai lamunci duk wani yunkuri na cin hanci da rashawa ba, abin da ya bayyana da zama cutar daji a kasar .

"Muna bukatar gwamnati mai inganci, haka kuwa abu ne da zai samu ta hanyar shugabanci nagari, wanda babu batun cin hanci da rashawa a cikinsa, abinda ke zame mana tamkar cutar daji wacce zamu tashi tsaye baki daya mu yi yaki da ita".

A ranar 24 ga watannan na Disamba ne dai shugaba Kiir ya rushe jihohi 10 na Sudan ta Kudu da samar da sabbin jihohi 28 a yunkurin da ke shan suka ta 'yan adawa.