Shugaba Kim da Moon za su gana
September 16, 2018Talla
Tuni hukumomin Koriya ta Arewa suka shirya tarbar tawagar Shugaba Moon Jae-in mai kawatarwa a babban filin sauka da tashin jiragen sama a birnin Pyongyang, dan halartar taron koli kan makamin nukiliya da takorarsa Kim Jung-un da aka shirya a ranar Talatar da ke tafe.
Wannan dai shi ne karo na uku da shugabannin za su gana da juna cikin shekarar 2018, sai dai sun gana a watan Afirilun da ta gabata a wani kauyen da ke kan iyakar kasashen biyu.
Ana sa ran ganawar za ta yi tasiri wajen inganta dangantaka tsakanin Koriyoyin biyu, bayan daukar tsawon lokaci ba a ga maciji da juna.