1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sauyin siyasar Faransa a Afirka

July 25, 2022

Shugaban Faransa na ziyarar aiki a wasu kasashe na Afirka, inda ya fara yada zango a Kamaru kafin ya je Jamhuriyar Benin da Guinea Bissau.

Brüssel  EU Afrika Gipfel  Mcron Rede
Hoto: Johanna Geron/AP/picture alliance

Wannan ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen da ta raina ke kara nuna wa Faransa kyama, lamarin da ya sa Macron ke yunkurin canja kamun ludayinsa game da manufinsa na Afrika.

Kasar Kamaru da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zaba wajen fara ziyararsa ya ba da mamaki, duba da cewa shugabanta Paul Biya na gudanar da salon mulkin sai Mahdi ka ture inda ya kwashe  shekaru 40 a kan kujerar mulki. Dama dai kasar ta Kamaru ta kwashe shekaru biyar tana fama da yakin basasa a lardunanta biyu da ke magana da turancin Ingilishi, lamarin da ya kasance a ajendar tattaunawa da shugaban Faransa ya yi da takwaran aikinsa Paul Biya, mai shekaru 89 da haihuwa.

Wani batu da ya dauki hankalin bangarorin biyu shi ne batun fursunonin siyasa da yadda ake amfani da karfi wajen murkushe boren masu amfani da Turancin Ingilishi na Kamaru. Amma Emmanuel Macron bai gana da dan hamayya Maurice Kamto kamar yadda aka shirya tun da farko ba. Wannan ya nuna cewa Macron ya sauya kamun ludayinsa, inda yake kauce wa tsoma baki a siyasar kasashen Afirka, a cewar Louis Keumayou, wani dan jarida kuma manazarcin siyasa na kasar Kamaru. 

Shugaba Paul Biya na KamerunHoto: picture-alliance/MAXPPP/B. Eliot

"Ina ganin cewa duk abin da ya shafi siyasar cikin gida, Macron zai ci gaba da yin taka-tsatsan. Ba zai dauki matsayi a hukumance ga wannan bangare ko wancan ba. Wannan ba wurin ko lokaci ne na nuna matsaya ba."

Ana ganin cewa dalilai na tattalin arziki ne suka sa Shugaba Macron ya kai ziyara Kamaru duk da rashin fahimta da ke tsakanin kasashen biyu. Wannan kasa mai al'umma akalla miliyan 25, wacce ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki a kungiyar Tattalin Afirka ta yankin Tsakiyar Afirka (CEMAC) a takaice, ta na iya kasancewa abokiyar hulda, a yanayin da Faransa ke bukatar karin makamashi sakamakon yakin Rasha da ukraine, kamar yadda Louis Keumayou ya bayyana.

"Tashar jiragen ruwa na Douala ta kasance kafar fitar da hajojin da ake oda daga ketare na kasashe biyu da Faransa ke da gagarumin matsayi a cikinsu: Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke da dangantaka da sojojin haya na Wagner, da Chadi da ke kokarin tattaunawa da 'yan tawaye don warware takaddamar siyasa da na soja. Sannan akwai batun kudin CFA, domin ba za iya tattaunawa kan ficewar Faransa daga tsarin kudin CFA a Afirka ta Tsakiya ba tare da tuntubar Kamaru ba."

Guinea Bissau na jerin kasashe uku da Emmanuel Macron na Faransa ke ya da zango a cikinsu, inda zai gana da shugaba Umaro Sissoco Embaló wanda kuma a daya hannun ke rike da ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar ECOWAS. Antoine Glaser, dan jarida kuma kwararre kan dangantakar Faransa da nahiyar Afirka ya ce sabon salon diflomasiyya da Faransa ta runguma a Afirka ya sa bi ta ECOWAS ya zama wajibi wajen cimma burinta.

Shugaba Umaro Embalo Guinea-Bissau Hoto: Iancuba Danso/DW

"Shugabancin kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO ne sabon makamin Emmanuel Macron. Faransa ta daina fitowa gaba gadi ta yi abin da take so, ko da a matakin soja ne. Idan Faransa na da muradin da take so ta kare, ko yaushe za ta rika bi ta kungiyoyin yankuna irin su ECOWAS."

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa na kallon rangadinsa na Jamhuriyar Benin a matsayin wata muhimmiyar rawa wajen karfafa makomar dimokuradiyya a nahiyar Afirka. A watan Oktoba mai zuwa, kasar Faransa za ta samar da gidauniyar inganta dimokuradiyya a Cotonou babban birnin Benin, karkashin jagorancin masanin kimiyyar siyasa Achille Mbembe. Dama a shekarar da ta gabata, masanin ya mika wa Emmanuel Macron wani rahoto kan makomar dangantaka tsakanin Faransa da Afirka.