Shugaba Macron zai gana da Putin a Moscow
February 7, 2022Talla
Shugaba Macron shi ne shugaba na farko daga kasashen yamma da zai yi ganawar keke da keke da Putin tun bayan da wannan rikici ya barke a watan Disamba shekarar da ta gabata.
Macron na fatan wannan tattaunawa da zai yi da Putin ta kawo karshen wannan rikicin da kasashen yamma ke ciki da Rasha wanda ba a ga irin shi ba tun bayan yakin chachar baka.
A gobe Talata kuma Mr. Macron zai isa birnin Kyiv na Ukraine inda a can ma zai tattauna Shugaba Volodmyr Zelensky, a kokarin da ake yi na ganin an rikcin cikin ruwan sanyi.
Wannan yunkuri na Macron dai na zuwa ne daidai lokacin da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ke ziyara a Amirka son ganawa da ShugabaJoe Biden a fadar mulki ta White House kan rikicin na Ukraine.