Shugaba Masisi ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasa
November 1, 2024Shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da ya gudana a ranar Laraba da ta gabata. Tuni ma dai ya gudanar da taron manema labarai a birnin Gaborone, inda ya yi wa bangaren adawa barka da arziki. Wannan sauyin shugabancin ya samu ne bayan da jam'iyyar BDP mai mulki a Botswana ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar dokokin kasar.
Karin bayani: Zaben Botswana: Masisi na neman wa'adi na biyu
Jaridar Mmegi ta ruwaito cewa kawancen jam'iyyun 'yan adawa ya lashe kujeru 36 daga cikin kujeru 61 da majalisar dokokin kasar ta tanada. Ita dai jam'iyyaar BDP Botswana (Democratic Party) na kan karagar mulki ne kusan shekaru 60 da suka gabata, lamarin da ke zaman karonsa na farko kenan da 'yan hamayya suka yi gagarumar nasara.