Shugaba Merkel za ta fara ziyara a Afirka
March 2, 2017A ranar Alhamis din nan ce Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta fara ziyara ta kwanaki biyu a kasashen Masar da Tunisiya a kokarinta na samun hadin kan shugabannin wadannan kasashe wajen ganin an takaita kwararar bakin haure da ke son danganawa da Turai daga Arewacin Afirka musamnman wadanda ke fitowa daga Libiya da yaki ya sa ta cikin rudani. Tun dai bayan hambarar da Moamer Kadhafi a shekarar 2011 kasar ta Libiya ta zama babban dandali da ke samun halartar baki daga kasashen Afirka da ke son danganawa da kasashe 28 mambobi na Kungiyar EU.
Shugaba Merkel dai da ke fuskantar kalubalen zabe a watan Satimba mai zuwa na ci gaba da fuskantar matsin lamba ta rage yawan baki yan gudun hijira da ke zuwa Jamus wandanda kasar tuni ta karbi sama da miliyan daya tun daga shekarar 2015. Gwamnatinta dai na bukatar mahukuntan a yankin Magrib su kula da iyakokinsu dan hana bakin sulalewa zuwa Turai kana su yi kokari wajen ganin an gaggauta karbar bakin da suka gaza samun mafakar siyasa a kasashen na Turai.
Merkel za ta fara ziyarar ce a Masar inda za ta gana da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi, kafin daga bisani a ranar Juma'a ta gana da Shugaba Beji Caid Essebsi na kasar Tunusiya.